India

Kisan yaro Dan shekaru 13 ya jawo bore a yankin Kashmir

Masu zanga zanga a yankin Kashmir
Masu zanga zanga a yankin Kashmir 照片来源:路透社

Kisan da ‘Yan sanda suka yi wa wani yaro a yankin Kashmir dake yankin kasar India, ya jawo bore wanda hakan yasa hukumomin kasar suka saka dokar hana zirga – zirga. Dan shekaru 13, Ubaid Mushtaq ya rasu ne a asibiti bayan an harbe shi a zanga zangar nuna kin amincewa da wani hukuncin kisa ta rataya da akawa dan kishin yankin Kashmir bayan an same hanunsa cikin harin da aka kai a majalisar kasar India a shekarar 2001. 

Talla

Akalla mutane 3,500 suka halarci jana’izar Ubaid a yayin da aka binne shi a kauyensa na Watergam wanda ke kusa da garin Sopore.

Rahotanni na nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a yankin Kashmir yayin da bankuna da shugunan kasuwanci suka kasance a rufe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.