Syria

An kai harin bom a ofishin jama'iyyar Bath mai Mulkin Siriya

Irin illar da yakin Siriya ya yi
Irin illar da yakin Siriya ya yi REUTERS/Muzaffar Salman

Wani harin Bam da aka kai a yau, kan cibiyar jam’iya Bath, mai mulkin kasar Syriya, da ke birnin Damascus ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 30.Jim kadan bayan, tashar Talibijin din gwamnatin kasar, ya ruwaito wasu sabbin hare haren da aka kai da rokoki, kan babbar hedkwatar sojojin kasar, dake Damascus Babban birnin kasar ta Syriya.Tashar Talibijin din ta Al Ekhbariya ta ce, daga cikin mutanen da suka jikkata a harin da aka kai a unguwar Mazraa, sun hada da yara kankana, da ke halartar wata makarantar da ke kusa da inda fashewar ta wakana.Hotunan da aka yada a Talibijin, din sun nuna irin barnar da fashewar ta haddasa. Inda aka nuna motocin da suka tarwatse suna cin wuta tare da gine ginen da suka rushe a wani dandali, kusa da masallacin al Imane dake cibiyar jam’iyar ta Bath mai mulki kasar ta Syriya, yau sama da rabin karni da ya gabatakungiyar kare hakkin dan adam ta OSDH a kasar, ta kara da cewa an kai wasu hare haren Bam a cikin motoci kan wasu shingayen binciken jami’an tsaro dake anguwar Barze arewacin birnin.watannin da dama da suka gabata ne dai, birnin Damas ke fama da hare haren Bam, wadanda suka yi sanadiyar hasarar rayukan jama’a da dama, kuma akasarinsu kungiyar yan tawayen Islamar kasar, ta dauki alhakin kaiwa.