India

Mutane 7 sun mutu a harin Kashmir a India

Ana kwasar daga cikin Jami'an tsaron da suka jikkata a harin Kashmir kasar India.
Ana kwasar daga cikin Jami'an tsaron da suka jikkata a harin Kashmir kasar India. REUTERS/Danish Ismail

Akalla ‘Yan sanda biyar ne suka mutu sakamakon wani hari da aka kai wa Jami’an tsaro a yankin Kashmir kasar India. Jami’an tsaron kasar sun ce sun samu nasarar kashe ‘Yan bindigar guda biyu daga cikin wadanda suka kai harin.

Talla

Wani Babban Jami’in ‘Yan Sanda ya tabbatar wa maneman labarai cewa ‘Yan sanda biyar ne suka mutu a harin da ‘Yan bindiga suka kai a yankin Benima.

An kai harin ne a kusa da barikin Sojoji kuma akalla ‘Yan sanda bakwai ne aka ruwaito sun jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.