Bangladesh

Firaministan Bangladesh ta yi watsi da bukatar kafa dokar batanci ga addini

Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina
Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina

Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina ta yi watsi da sabuwar dokar da ke neman hukunta wadanda suka ci mutuncin addinin Islama duk da fatawar da masu kishin Islama ke yi na ganin an kaddamar da dokar domin yanke hukuncin kisa ga wadanda suka ci mutunci musulunci da kuma Manzon Allah.

Talla

A wani mataki na kokarin an tabbatar da dokar, kungiyar musulmi ta Hefajat-e-Islam ta sa an rufe makarantu da masana’antun kasar tare da dakile zirga-zirga.

‘Yan sanda sun ce akalla sama da mutane 30 ne suka samu rauni a zanga zanga tsakanin magoya bayan gwamnati da kuma masu kishin Islama.

Amma Sheikh Hasina, da ke jagorancin gwamnatin da babu ruwanta da addini a kasar Bangladesh mai yawan mabiya Addinin Musulunci tace dokokin kasar sun isa a hakunta duk wanda ya ci mutuncin addini.

A hirar ta da kafar yada labaran Birtaniya, Hasina tace ba su bukatar wani tsari da zai samar da sabuwar doka.

A ranar Assabar, dubban mabiya addinin Islama ne suka fito saman tituna suna zanga-zanga a birnin Dhaka domin bukatar ganin an kafa sabuwar dokar da za ta bayar da damar yanke hukuncin kisa ga duk wanda ya ci Mutuncin Addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI