Korea-Amurka

China da Amurka za su kwance wa Korea ta Arewa damarar nukiliya.

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un
Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un Reuters

Bayan wata doguwar tattauna da suka yi a birnin Beijing a yau asabar, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na China Yang Jiechi, sun ce kasashen za su yi aiki kafada-da-kafada domin kwancewa Korea ta Arewa damarar nukiliya amma ta hanyar yin amfani da hanyoyi na diplomasiyya.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan wannan ganawa cewa, kasashen za su yi iya kokarinsu domin gaggauta samun nasarar hakan, inda ya ce kasashen biyu na shirin gudanar da wani taro a nan gaba domin ci gaba da tattaunawa dangane da wannan batu.
Ministan harkokin wajen kasar China Yang, ya ce kasarsa a matsayinta wadda ke da kyakkyawar alaka da hukumomin Pyongyong, za ta yi dukkanin abin da ya kamata domin kawo karshen barazanar yin amfani da makakaman nukiliya da Korea ke yi wa Amurka da kuma wasu kasashen yankin da ake kallo a matsayin kawayen Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI