Pakistan

Kotu a Pakistan ta tsawaita kariyar da ta bai wa tsohon shugaba Musharraf

Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf
Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf Reuters

Kotun kasar Pakistan a jiya juma’a ta kara tsawaita batun bada belin tsohon shugaban kasar ta Pakistan Pervez Musharraf a wani zama da ta yi a cikin tsauraran matakan tsaro.

Talla

Janar mai ritaya da a ranar 24 ga watan jiya ya sake tsoma kafarsa a kasar bayan share shekaru 4 yana gudun hijira, Musharraf na da niyyar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a ranar 11 ga watan Mayu mai zuwa, ya kuma yi koma Pakistan ne duk kuwa da barazanar kashe shi da kungiyar Taliban ta yi, kuma a karon farko ya halarci zaman kotun a jiya cikin tsauraran matakan tsaro.

Ana dai zargin Pervez Musharraf ne da alhakin kisan shugaban ‘yan awaren yankin Balustchita da ke kudu maso yammacin kasar Akbar Bugti, da tsohuwar PM kasar Benazir Bhutto da kuma daure wasu manyan alkalai na kasar a lokacin mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI