Korea-Amurka

Amurka da Japan za su hana Korea ta Arewa mallakar makaman nukiliya

John Kerry da kuma ministan harkokin wajen Japan
John Kerry da kuma ministan harkokin wajen Japan REUTERS/Issei Kato

Kasashen Amurka da Japan sun cimma jituwa kan hana Korea ta Arewa mallakar makaman Nukliya.Ministan harkokin wajen Amurka John Kerry ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da takwaran aikinsa na kasar Japan a ci gaba da ziyarar aikin da yake yi a kasashen Asiya.

Talla

Suna daukar wannan matakin ne a bayan takunkumman da aka kakabawa kasar ta Korea ta Arewa kan gwajin makamin Nukiliyar da ta yi, abin da ya sake yada jita-jitar cewar da wuya idan har Korea ta Arewar ba da niyyar sake gwajin wani sabon makamin Nukiliya a cikin kwanaki masu zuwa.
Ko a jiya assabar ma sakataren na harkokin wajen Amurka ya tattauna da wasu manyan jami’an gwamnatin China a kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI