Pakistan

Musharraf ya gurfana a gaban kotun Pakistan akan zargin kisan Bhutto

Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf bayan ya gurfana a gaban Kotu
Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf bayan ya gurfana a gaban Kotu Reuters

Tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf ya gurfana a gaban kotun kasar a karo na farko game da zargin kisan tsohuwar Firaminista Benazir Bhutto a zamanin Mulkin shi na soji.

Talla

An kwashi Musharraf ne zuwa kotun kasar da ke hedikwatar Soji a Rawalpindi daga gidansa da ke Islamabad.

Ana zargin Musharraf ne da hannu wajen kisan Bhutto da aka kashe da harsashen bindiga a watan Disemba shekarar 2007.

Wannan zargin dai shi ne na uku da tsohon shugaban ke fuskanta tun bayan da ya dawo gida Pakistan daga gudun hijira ta kashin kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI