Afghanistan

Jami'an kungiyar NATO 3 sun mutu a Afghanistan

Wasu dakarun kungiyar NATO, da ke aiki a Afghanistan
Wasu dakarun kungiyar NATO, da ke aiki a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani

A yau Asabar wasu jami’ai 3, da ke aiki da kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN a kasar Afghanistan, suka mutu a wasu tashe tashen hankula. Kungiyar ta NATO tace mutanen, da suka hada da farar hula 1, sun mutu ne a wurare daban daban a yankin gabashin kasar, mai fama da tashe tashen hankula.Ya zuwa yanzu jami’an kungiyar ta NATO 71 ne suka mutu a kasar ta Afghanistan, ciki shekarar 2013, da suka hada da 26 da suka mutu cikin watan Mayu.Duk wannan na faruwa a daidai lokacin da harkokin tsaron kasar ke ci gaba da komawa hannun sojan kasar, kafin janyewar dakarun kasashen waje, a shekara mai zuwa ta 2014.