Pakistan

Sojoji 3 da mayakan sa kai 34 ne suka mutu a kasar Pakistan

Wani sojan kasar Pakistan yana sintiri
Wani sojan kasar Pakistan yana sintiri REUTERS/Naseer Ahmed

Akalla Sojin sa kai 34 da Dakarun kasar Pakistan 3 ne suka mutu a wani tashin hanakalin daya faru a kasar ta Pakistan.Wannan dai ya faru ne sakamakon bata kashi, da akayi a wani yanki da Sojin kasar ke kula da shi.Kuma ya faru ne a wani wuri dake tsakanin yankin Kurram da Khyber a cikin kauyukan Para Chankani da Maidan, a lokacin da Sojin ke sintiri domin kawar da ‘ya’yan kungiyar Taliban.Akalla dai an kwashe Wuni daya ana musayar harbe harbe tsakanin Sojin da ‘yan tawayen yankin.