Syria

Wani dan kasar Britaniya ya mutu a yakin Kasar Syria

Wasu 'yan tawayen kasar Syria suna fafatawa da sojan Gwamnati
Wasu 'yan tawayen kasar Syria suna fafatawa da sojan Gwamnati Reuters

Wani sabon rahoton da aka fitar ya nuna cewar an kashe wani dan kasar burtani a yakin da ake gwabzawa a kasar Siriya.Wannan ya biyo bayan da Soji suka bayyana kisan wasu mutane 3 yan kasashen waje Turawa, abinda ya nuna cewar wancan zargin da ake cewar ‘yan kasashen waje na fada tare da ‘yan tawayen kasar domin kawar da shugaba Bashar al-assad gaskiya ne.Hukumomi a kasar ta burataniya dai sun tabbatar da kisan dan kasar kuma an sanar da iyalan mamacin.Yakin na kasar ta Siriya, da aka shafe fiye da shekaru 2 ana gwazawa, ya lakume rayukan mutane da dama.