China/Sin

Gobara ta kashe mutane 119 a Sin

A kasar China akalla mutane kusan 119 aka ruwaito sun mutu sakamakon wutar gobara da ta tashi a wani gidan kaji a yankin Jilin.   

Talla

Rahotanni masu karo da juna da ke fitowa daga China na cewa an samu barkewar gobarar ne sakamakon fashewa, a yayin da kuma wasu rahotannin ke cewa an samu gobarar ne daga matsalar wutar lantarki.
An danganta wannan gobarar a matsayin gobara mafi muni a kasar china tun shekarar 2000 da aka samu wata gobararar wuta da aka samu hasarar rayuka kimanin 309 a yankin Henan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.