Philippine

An rufe filin jiragen sama na Manila, a Philippines

Dogayen gine-gine dake Manila na kasar Philippines
Dogayen gine-gine dake Manila na kasar Philippines rfi

Hukumomi a kasar Philippines sun umarci a rufe babban filin jiragen saman kasar dake Manila sakamakon wani tsautsayi da aka samu a lokacin da wani jirgin sama na fasinja  ya nemi zarce hanyar sa na sauka.Hukumar kula da filayen jiragen saman kasar tace za’a rufe filin na tsawon yau.Wannan jirgin sama na fasinja na dauke da mutane 165 a lokacin daya nemi sauka cikin yanayin ruwan sama.Dukkan fasinjojin sun fita babu wanda ya sami rauni bayan da wannan jirgi ya zarce inda aka tsara zai bi ya tsaya.