Iran

Jagoran kasar Iran ya ce ba sauyin siyasar da za a sama bayan zaben kasar

jagoran juyin musulunci a Iran, Ayatullah Ali Khamenei
jagoran juyin musulunci a Iran, Ayatullah Ali Khamenei

Jagoran juyin juya hali na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce babu wani sauyi da za’a sama a duk wanda ya lashe zaben shugabancin kasar game da tankiyar da ke tsakanin gwamnatin Iran da kasashen Turai, yana mai cewa Iran tana nan kan matsayinta na bunkasa shirinta na Nukiliya.

Talla

Kalamansa dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin shiga zaben shugaban kasar a ranar 14 ga wannan wata na Yuni domin samun shugaban da zai karbi mukami daga hannun Mahmoud Ahmadinejad, wanda wa’adinsa ke gaf da kawo karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI