Syria

Dakarun gwamnatin Syria sun kwace Qusayr daga hannun 'yan tawaye

Wasu gidaje bayan gumurzun da aka yi a Syria
Wasu gidaje bayan gumurzun da aka yi a Syria Trad al-Zouhouri/Shaam News Network/Handout via Reuters

Rahotanni daga kasar Syria, na nuni da cewa dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan mayakan kungiyar Hizbiullah, sun samu nasarar kwace birnin Qusayr da ke kusa da iyakar Labanan daga hannun ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan kasashen ketare.

Talla

Kwace birnin dai ya biyo bayan dauki ba dadin da aka kwashe makwanni uku ana yin e a tsakanin bangarorin biyu, inda rahotanni ke cewa an kashe mutane masu tarin yawa a lokacin wannan artabu.

Gidan talabijin mallakar gwamnatin Syria ya sanar da cewar, yanzu haka Qusayr da ke lardin Homs, ya koma hannun dakarun Gwamnati, kuma an kashe Yan Tawaye da dama a fafatawar da aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI