Faransa

Shugaba Hollande na Faransa ya kai ziyara Japan

Shugaban Faransa François Hollande yayin da ya isa kasar Japan
Shugaban Faransa François Hollande yayin da ya isa kasar Japan

Shugaban Faransa Francois Hollande ya isa kasar Japan domin ziyarar kwanaki 3, inda ake sa ran zai sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan makamashin Nukiliya da zirga zirgar jiragen sama tsanin faransa da Japan. Ziyarar na zuwa ne makoni 3 bayan da shugaban ya ziyarci kasar Sin, kuma ita ce ta farko da wani shugaban Faransa ya kai Japan cikin shekaru 17.Shugaba Hollande, da ministocin shi da ma ‘yan kasuwar da ke cikin tawagar tashi, sun isa Japan din da fatan ganin dabarun da Prime Minista Shinzo Abe ke shirin dauka, na farfado da tattalin arzikin kasar, da baya da karsashi a baya bayan nan.Ministocin Faransa 6 ne suka yi wa Hollande rakiya, da suka hada Ministan harkokin waje Laurent Fabius da takwaran shi na ma’aikatar bunkasa masana’antu Arnaud Montebourg, tare da Jagororin wasu kamfanonin Faransa 40, da suka hada da shugaban Kamfanin Areva.Ana sa ran kasashen 2 za su sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa kan makamashin na Nukiliya, a yayin da PM Abe yace zai bayar da umarnin sake bude cibiyoyin Nukiliyan kasar da aka rufe, da zaran an tabbatar da rashin illar su, duk kuwa da dari darin da ‘yan kasar ke yi kan hakan, sakamakon bala’ind da ya afka wa cibiyar Nukiliya ta Fukushima, shekaru 2 da suka wuce.