Saudiya-Syria

Saudiya ta ba ‘Yan tawayen Syria izinin jagorantar mahajjata

Zauren Majalisar Shura a kasar Saudiya
Zauren Majalisar Shura a kasar Saudiya Reuters/Ali Jarekji

Gwamnatin Saudiyya ta ba gwamnatin ‘Yan tawayen Syria izinin jagorantar kula da ‘Yan kasar da ke bukatar sauke farali a Hajjin bana, wanda hakan ke nuna Saudiya tana goyon bayan ‘Yan tawayen da ke ci gaba da yaki da gwamnatin shugaba Bashar Assad.

Talla

A bara, Saudiyya ce ta dauki hidimar tattantace mahajjantan Syria ba tare da neman taimakon gwamnatin Assad ba.

Kakakin ma’aikatar kula da aikin Hajjin Saudiya, Hatem Qadi ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewar Saudiya ta mika ragamar kula da aikin hajji ga ‘Yan tawayen Syria, yana mai cewa Saudiya ta dauki matakin ne bayan wakilan ‘Yan tawayen sun gana da mahukuntan kasar.

A watan Oktoba ne dai za’a gudanar da aikin Hajjin bana.

A bara gwamnatin Syria ta zargi Saudiya da haramtawa mahajjan kasarta sauke farali, zargin da Saudiya ta musanta.

Tuni dai gwamnatin Saudiya ta katse hulda da gwamnatin Syria tare da kiran Shugaba Bashar al Assad ya yi murabus saboda jubar da jini da ake ci gaba da yi tsakanin shi da ‘Yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI