Syria

Iran ta ce an gayyace zuwa taron Geneva kan kasar Syria

Sojoji masu bayayya ga shugaban Assad na Syria
Sojoji masu bayayya ga shugaban Assad na Syria REUTERS/Mohammed Azakir

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdullahian, ya ce kasarsa ta samu goron gayyata domin halartar tattaunawar da kasashen duniya za su gudanar kan rikicin kasar Syria wanda zai gudana a birnin Geneva.

Talla

Ministan ya ce kasarsa, ta samu goron gayyatar ne yau kusan kwanaki 10 da suka gabata, inda ya ce halartar Iran a taron, za ta taimaka wajen samun nasarar.
Tun da jimawa ne dai kasar Rasha, ta bukaci kasashen duniya da su bai wa Iran, wadda babbar aminiya ce ga shugaba Assad, damar halartar wannan tattaunawa ta birnin Geneva.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI