Syria

Hoton bidiyo ya nuna ‘Yan tawayen Syria na murnar kashe 'yan Shi’a

Wani gida da da aka kai wa hari a syria inda masu sa ido suka kai ziyara
Wani gida da da aka kai wa hari a syria inda masu sa ido suka kai ziyara Reuters

Wani hoton Bidiyo da aka fitar ya nuna wani bangare na ‘Yan tawayen Syria da suka kira kansu mabiya Sunni suna murnar kashe mabiya Shi’a 60 da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar Assad tare da kona gidajensu a gabacin kasar.

Talla

Bidoyon wanda Kungiyoyin da ke lura da rikicin Syria suka yada, an fitar da shi ne bayan samun rikicin banbancin akida tsakanin Mabiya Sunni da Shia a kauyen Deir Ezzor, wanda hakan ke nuna rikicin Syria yana neman ya rikide zuwa rikicin banbancin akida.

A cikin hoton Bidiyo an ji kalaman wani mai daukar hoto yana cewa a shirye ‘Yan tawaye suke su kona gidajen mabiya shi’a saboda goyon bayan da suke ba gwamnatin Bashar Assad.

Wani hoton bidiyon kuma ya nuna ‘Yan tawayen rike da makamai, hayaki na tashi a gidajen da suka kona.

Yawancin Mutanen Syria dai mabiya Sunni ne amma kabilar Alawite ta Assad ta kwashe tsawon shekaru 40 tana shugabancinsu, wadanda kuma mabiya Shi’a ne "Alawiya".

Taimakon da Bashar Assad ke samu daga kungiyar Hezbollah ta Lebanon shi ke kara hura wutar rikicin Syria, musamman taimakon da suka ba dakarun Assad wajen karbe ikon birnin Qusayr.

Yanzu haka kuma rahotanni sun ce dakarun Assad sun doshi Homs domin ci gaba da karbe iko daga hannun ‘Yan tawaye.

Shigar Hezbollah a Syria, shi ne matakin da ya sa ‘Yan Tawayen kasar ke ci gaba da samun goyan baya daga kasashen Duniya, inda Hukumomin Faransa suka yi kira domin taimakawa ‘yan Tawayen da makanmai bayan kungiyar Turai ta janye takunkumin shigar da makaman ga ‘Yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.