Iran

An fara zaben Shugaban kasa a Iran

Jamian zabe a kasar Iran suna karba kayan aiki
Jamian zabe a kasar Iran suna karba kayan aiki rfi

A kasar Iran, fiye da mutane milyan 50  ke jefa kuri’unsu a yau  Juma’a, domin zaben wanda zai maye gurbin Shugaba Mahmud Ahmadinejad, a tsakanin ‘yan takara  shida  da ke neman hawa kujeran Shugabancin kasar.Alhaji Abubakar Cika, tsohon jikadan Tarayyar Najeriya a kasar ta Iran, ya yi wa sashen Hausa na RFI bayani gameda wannan zabe mai muhimmanci a kasar Iran. Tun da sanyin safiya dafifin jama'a maza da mata suka yi layi a tashoshin jefa kuri'u dake sassan kasar.Babu mace ko daya da aka amince ma ta ta shiga wannan takara, wanda Shugaba Mahmud Ahmadenajad bashi da ikon tsayawa domin ya kammala wa'adinsa biyu.Jagoran addini na kasar Ayatollah Ali Khomenei bai fito fili na nuna dan takara daya da yake goyon baya ba, sai dai kawai yace "insha Allah zaben za'ayi nasara", jim kadan bayan ya jefa kuriarsa