Bakonmu A yau: A game da zaben kasar Iran

Sauti 03:40
Jami'an zabe a kasar Iran.
Jami'an zabe a kasar Iran. (©Reuters)

A ranar juma'a 14 ga watan Yuni, an gudanar da zaben shugaban kasa a Iran, a daidai lokacin da Mahmoud Ahmadinejad ke shirin kawo karshen wa'adin mulkinsa na shekaru 4. A wannan zabe dai, akwai 'yan takara 6 daga bangarori biyu na siyasa, wato masu ra'ayin rikau da kuma masu ra'ayin samar da sauyi.Alhaji Abubakar Cika, tsohon jikadan Tarayyar Najeriya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal, yadda yake kallon wannan zabe da kuma muhimman batutuwan da ke gaban sabon shugaban da za a zabawa kasar.