Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila tace samun ‘Yancin Falesdinawa mataccen zance ne

Benyamin Netanyahu, Firaministan kasar Isra'ila
Benyamin Netanyahu, Firaministan kasar Isra'ila REUTERS/Abir Sultan/Pool

A dai dai lokacin da kasar Amurka ke cewa tana iya kokarinta don sake farfado da tattaunawar zaman lafiya da nufin samar da kasashen biyu wato Isra’ila da kuma Falasdinu, da za su rayu kafada da kafada, Ministan tattalin arzikin kasar Isra’ila Naftali Bennett ya ce wannan ‘’mataccen zance ne’’.

Talla

Kalaman na minista Bennett, maimaici ne ga wadanda ya taba furtawa a lokacin da ya ke yakin neman zabensa a cikin watan Janairun da ya gabata, yayin da Amurka ke cewa tana iya kokarinta domin farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da kuma Yahudawan Isra’ila.

Ministan tattalin arziki, ya ce samuwar kasar Palasdinu mataccen zance, kuma muhimman abin da ke gaban Isra’ila, shi ne ci gaba da aiwatar da gine gine a kan kasar yahudawa ta asali.

Jagoran tawagar Palasdinu a tattaunawa da Isra’aila Sa’eb Erakat, ya bayyana kalaman na ministan tattalin arziki da cewa wani koma baya ne ga yunkuri samar da zaman lafiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI