Afghanistan

An kai wani munmunan hari a Kabul

Dakarun tsaron NATO a Afghanistan
Dakarun tsaron NATO a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani

Wani Dan kunar bakin a kasar Afghanistan, ya tayar da bom a kusa da gidan wani fitattacen Dan Majalisa, Haji Mohammed Mohafiq, wanda ya hallaka mutane uku. Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake saran kungiyar NATO za ta mika ragamar tafiyar da tsaro ga jami’an tsaron Afghanistan.

Talla

Rahotanni sun ce dan majalisar bai samu rauni ba amma kimanin mutane shida ne suka samu rauni.

A kokarin ficewa daga Afghanistan, dakarun NATO zasu mika ragamar tafiyar da tsaro daga sauran yankunan da ke karkashin ikonsu, a bukin da Hamid Karzai da kwamandan tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen za su jagoranta.

Wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da ake saran kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan, za ta bude ofishinta na diplomasiya a birnin Doha, da ke kasar Qatar. Gidan talabijin din Aljazeera ya ruwaito cewar wani daga cikin shugabanin kungiyar ne ya tabbatar da haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI