Malam Hafiz Muhammad Dalibi a Jami'ar Qum a kasar Iran

Sauti 03:25
Zababben Shugaban kasar Iran Hassan Rohani a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tehran
Zababben Shugaban kasar Iran Hassan Rohani a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tehran REUTERS/Fars News/Majid Hagdost

Shugaban kasar Iran mai jiran gado, Hassan Rohani yace gwamnatin shi ba za ta dakatar da shirin Iran na sarrafa sinadarin Nukiliya ba, duk da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba kasar a baya. Rohani mai sassaucin ra’ayi ya yi alkawarin tattaunawa da kasashen duniya kan batun ba tare da rufa rufa ba. Malam Hafiz Muhammad da ke karatu a jami’ar birnin Qum a kasar ta Iran, ya yi wa Nasirudden karin bayani kan kalaman na Sheik Rohani.