Ra'ayin masu saurare game da Tattaunawar Amurka da Taliban

Sauti 20:01
Zauren tattauna da Kungiyar Taliban ta Afghanistan a birnin Doha, kasar Qatar
Zauren tattauna da Kungiyar Taliban ta Afghanistan a birnin Doha, kasar Qatar REUTERS

Gwamnatin Afghanistan ta katse tattaunawa da Amurka saboda sabanin ra’ayi tsakanin kasashen biyu game da tattaunawa da Kungiyar Taliban. Shugaba Hamid Karzai ya yi watsi da duk wani yunkuri na tattaunawa da Taliban idan ba karkashin jagorancin Afghanistan ba ne. wannan kuma na zuwa ne bayan Taliban ta bude ofishinta a Birnin Doha na kasar Qatar. Masu sauraren RFI hausa sun bayyana ra’ayinsu game da wannan batu tare da Faruk Yabo.