Amurka-Afghanistan

Gwamnatin Afghanistan na adawa da buda ofishin Taliban a Qatar

Muhammad Naeem, jami'in jikadancin Taliban a kasar Qatar
Muhammad Naeem, jami'in jikadancin Taliban a kasar Qatar REUTERS/Mohammed Dabbous

Kasar Qatar ta ce ofishin Jakadancin kungiyar Taliban da aka bude a Doha dan tattaunawa, ba shi da nasaba da sunan Jamhuriyar Islamar Afghanistan, wadda shugaba Hameed Karzai ke korafi a kai.

Talla

Shugaba Karzai ya bayyana cewar takala ce, yadda kungiyar ta sanya sunan gwamnatin da aka hambarar da ita a shekarar 2001 ta ‘yan Taliban, matakin da ya sa aka soke tattaunawar Afghanistan da kuma gwamnatin Amurka.

Tun da jimawa ne dai kasar ta Qatar da kuma Amurka suke kokarin ganin cewa kungiyar ta Taliban wadda Amurka da kawayenta ke kallon a matsayin ta ‘yan ta’adda, ta buda ofishinta a Qatar domin sawwaka tattaunawar samar da zaman lafiya da ita, lamarin da Kabul ke yin dari-dari da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI