Syria

Assad ya karawa Sojojin shi albashi

Wani dauke da hoton Shugaban Syria Bashar al Assad
Wani dauke da hoton Shugaban Syria Bashar al Assad REUTERS / Khaled Abdullah

Shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya bayar da umurnin karawa Sojoji da ma’aikata albashi, a wani yunkuri na samar da kariya ga masu goyon bayan gwamnatin shi daga matsalar  hauhawan farashin abinci saboda yakin basasa a kasar.

Talla

A cewar Kamfanin Dillacin labaran SANA, sojoji da ma’aikata zasu samu karin albashi na kashi 40 daga kudin albashinsu. Haka kuma za’a kara masu kudaden Fansho.

Wannan ne dai karo na biyu da gwamnatin Assad ke karawa Sojoji da ma’aikata Albashi tun kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin shi a watan Maris din shekarar 2011.

An dai samu faduwar darajar kudin kasar Syria, tsawon watanni 27 da aka kwashe ana gwabza yaki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI