Syria-Qatar

Taron kawayen Syria a Doha

Wakilin gwamnatin Qatar Ibrahim Fakhroo yana tarbon Jekadaiyar Amurka a Qatar Susan Ziadeh tare da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry bayan sun sauka a birnin Doha
Wakilin gwamnatin Qatar Ibrahim Fakhroo yana tarbon Jekadaiyar Amurka a Qatar Susan Ziadeh tare da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry bayan sun sauka a birnin Doha REUTERS/Jacquelyn Martin/Pool

Ministocin harkokin wajen kasashen da ke kiran kansu aminnan Syria na gudanar da taro a birnin Doha na kasar Qatar domin duba sabbin hanyoyin taimakawa ‘yan tawaye da Makamai don kawo karshen gwamnatin Bashar al Assad.

Talla

Kwana daya kafin buda wannan taro, mai Magana da yawun daya daga cikin kungiyoyin’yan tawayen Louay Muqdad, ya shaidawa manema labarai cewa sun samu Karin manyan makamai a cikin ‘yan kwanakin nan, kuma tuni suka soma raba wa magoya bayansu domin kaddamar da wani hari da nufin kifar da gwamnatin Bashar Assad.

Sakataren harakokin Wajen Amurka John Kerry, yana cikin manyan jami’an Diflomasiya da suka halarci taron na kawayen Syria.

Sai dai kuma gabanin taron Sakataren harakokin wajen Birtaniya William Hague wanda yanzu haka ke birnin Doha yace har yanzu babu matsaya da gwamnatinsu ta cim ma domin taimakawa ‘Yan tawayen Syria da makamai.

Amma tuni Amurka ta yi alkawalin taimakawa ‘Yan tawayen da makamai bayan tabbatar da binciken lallai Shugaba Bashar Assad ya yi amfani da makamai masu guba ga ‘Yan tawaye.

Kodayake babu wani bayani game da irin makaman da amurka za ta ba ‘Yan tawaye amma Jaridar Los Angeles Times ta ruwaito cewa dakarun Amurka sun kwashe watanni suna ba ‘Yan tawayen horo.

Taron kawayen na Syria, ana sa ran zai kunshi wakilai daga Masar da Faransa da Jamus da Italiya da Jordan da Qatar da Saudiyya da kuma Daular Larabawa.

Daga cikin batun da taron zai mayar da hankali, shi ne batun da Faransa zata jagoranta na hada gidauniya domin taimakawa ‘Yan tawayen na Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.