Pakistan
Pakistan tana tuhumar Musharraf da laifin cin amanar kasa
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Kasar Pakistan tace zata tuhumi tsohon shugaban kasa, Parvez Musharraf da laifin cin amanar kasa, mai dauke da hukuncin kisa. Fira Minista, Nawaz Sharif ne ya bayyana haka a Majalisa, inda ya ke cewa ya zama wajibi ga tsohon shugaban ya amsa laifin juyin mulkin da yayi, da kuma daure alkalai a kotu.