Afghanistan

Kungiyar Taliban ta kai hari Fadar Shugaba Karzai a Kabul

Jami'an tsaron Afghanistan suna gudu zuwa inda aka kai hari hari a kusa da fadar shugaban kasa a birnin Kabul
Jami'an tsaron Afghanistan suna gudu zuwa inda aka kai hari hari a kusa da fadar shugaban kasa a birnin Kabul REUTERS/Omar Sobhani

Rundunar ‘Yan Sandan Afghanistan tace ta kashe daukacin ‘Yan bindigar da suka kai hari fadar shugaba Hameed Karzai da safiyar Litinin. Shugaban ‘Yan Sandan Kabul, Mohammed Ayoub Salangi, ya shaidawa manema labarai cewar an kashe ‘Yan bindigan guda hudu, wadanda suka fice daga cikin motar su mai shake da bom, kafin ya tashi.

Talla

An kwashe sa’o’I ana jin karar harbin bindiga da kuma harin bom na farko wanda ya tashi da misalin karfe 6:30 na safe.

Harin dai na zuwa ne kafin Shugaba Hamid Karzai ya gana da manema labarai a fadar shi.

Tuni dai Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI