Syria-MDD

Susan Rice ta yi suka ga kwamitin tsaro game da Syria

Mai shiga tsakanin rikicin Syria Lakhdar Brahimi tare da sakataren harakokin siyasar Amurka Wendy Sherman a lokacin da suka tattauna batun Syria a Geneva
Mai shiga tsakanin rikicin Syria Lakhdar Brahimi tare da sakataren harakokin siyasar Amurka Wendy Sherman a lokacin da suka tattauna batun Syria a Geneva REUTERS/Fabrice Coffrini

Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, Susan Rice, ta yi kakkausar suka ga kwamitin Sulhu na majalisar kan rashin daukar matakin magance rikicin Syria, inda ta bayyana shi a matsayin abin kunya.

Talla

Sabuwar mai bai wa Obama shawara kan harkokin tsaro, Rice tace rashin samun hadin kai wajen daukar mataki kan Syria, zai zama wani tabo da ba za ta taba mantawa ba a rayuwar ta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaransa na Russia, Sergei Lavrov, zasu gana a makon gobe, don nazarin halin da ake ciki a Syria. Matakin na daga cikin shirin wani yunkuri na gudanar da taron zaman lafiya akan Syria.

A daya banagren kuma, mai shiga tsakani na Majalisar kan rikicin Syria, Ladkhar Brahimi, yace da wuya a iya gudanar da taron zaman lafiya a watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI