Isra'ila-Falesdinawa

Netenyahu zai rufe wasu matsugunan Yahudawa nan ba da jimawa ba

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu REUTERS/Abir Sultan/Pool

Fira ministan Isra’ila Bejamin Netenyahu, ya ce zai kaddamar da wani gagarumin shiri da zai tanadi rufe wasu matsugunan Yahudawa ‘yan kama wuri zauna, domin cika alkawalin da gwamnatinsa ta dauka karkashin shirin samar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da Palasdinawa.

Talla

Jaridar Washington Post, ta jiyo wani babban jami’in diplomasiyya na Isra’ila na cewa, tuni Fira ministan ya amince da wannan shiri a daidai lokacin da ake jiran isar Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry a birnin Jerusalem domin gudanar da ziyarar aiki.
Kerry, wanda ke ziyarar kasashen Larabawa karo na biyar daga lokacin da aka nada shi a kan wannan matsayi, a jiya ya kasance a kasar Jordan wadda ke taka gagarumar rawa a wannan batu na Palasdinawa da Isra’ila, inda kuma ya bayyana cewa zai matsa wa gwamnatin Netenyahu lamba domin samar da zaman lafiya da Palasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI