China ta kafa dokar ziyartar iyaye
Wallafawa ranar:
Kasar China ta fara aiki da wata dokar da za ta tilastawa matasan kasar ziyartar mahaifansu, sabanin yadda ake samu yanzu haka. Rahotanni sun ce, matasa a China ba su ziyartar mahaifansu, kuma akasarin mutanen kasar sun haura shekaru 60, matakin da ya zaburar da gwamnati daukar matakin. Sai dai ‘yan kasar sun yi ta sukar sabuwar dokar.