Indonesia

Mutane 22 sun mutu sakamakon Girgizan kasa a Indonesia

Kungiyoyin agaji suna aikin ceto sakamakon girgizan kasa mai karfin maki 6.2 da ta shafi Indonesia
Kungiyoyin agaji suna aikin ceto sakamakon girgizan kasa mai karfin maki 6.2 da ta shafi Indonesia REUTERS/Stringer

Hukumomin Kasar Indonesia sun ce girgizar kasar da aka samu a kasar, ya hallaka mutane 22, kuma sama da mutane 200 sun samu raunuka a Yammacin tsibirin Sumatra. Rahotanni sun ce, wasu yara shida sun mutu a cikin Masallacin Aceh, yayin da 14 kuma suka makale a ciki. Yanzu haka ana ci gaba da aikin ceto a kasar.