‘Yan sandan China sun bindige wani dan kabilar Tibet

'Yan kabilar Tibet da ke karrama shugabansu Dalai Lama
'Yan kabilar Tibet da ke karrama shugabansu Dalai Lama

‘Yan sandan china sun budewa ‘Yan kabilar Tibet wuta a lokacin da suke bukin taya shugabansu Dalai Lama cika shekaru 78 na hauhuwa. Kungiyoyin kare muradun Tebet sun ce an samu mutuwar mutum guda kuma wasu da dama ne suka samu rauni.

Talla

‘Yan sandan sun tarwatsa ‘Yan Tibet ne a yankin Sichuan a lokacin da suke karrama shugabansu wanda gwamnatin China ke adawa da shi.

Amma mahukuntan kasar sun karyata zargin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.