An yanke wa wani shugaban Jam’iyyar Musulmi hukuncin kisa a Bangladesh
Wallafawa ranar:
Kotun kasar Bangladesh ta yanke wa Ali Ahsan Mohammad Mujahid daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Jama’atul Islami hukuncin kisa bayan kama shi da laifin aikata laifukan yaki a lokacin samun ‘Yancin kasar daga Pakistan.
Kotun ta kama Mujahid da laifuka guda biyar da suka da sacewa da kisan mutane.
Mai shari’a Obaidul Hassan, ya bayar da umurnin a rataye Mujahid bayan an karanta hukuncin a zauren Kotun ta Musamman da ke Dhaka babbar Birnin Bangladesh.
Mujahid, shi ne mutum na biyu a cikin jerin sahun shugabannin Jam’iyyar Jama’atil Islami. Kuma wannan hukuncin shi ne irinsa na biyu a cikin mako guda bayan an yanke wa shugaban Jam’iyyar Ghulam Azam hukuncin daurin shekaru 90 a gidan yari.
Hukuncin Kotun dai ya sake hura wutar rikicin Bangladesh inda magoya bayan Jam’iyyar Jama’at suka fito saman tituna suna gudanar da zanga-zangar adawa da hukuncin da Kotun ke yake wa Shugabanninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu