Amurka-Syria-Rasha

Syria ta tabbatar da shirin sayen makamai daga Rasha

Mataimakin Praministan kasar Syria Qadri Jamil
Mataimakin Praministan kasar Syria Qadri Jamil 照片来源:路透社REUTERS/Maxim Shemetov

Syria tace har yanzu shirin sayen makaman da take yi a hannun kasar Rasha yana nan daram, duk da sukar da kasashen duniya ke yi. Mataimakin Fira Ministan kasar ta Syria, Qadri Jamil ne ya bayyana haka, bayan ganawar da yayi da ministan harkokin wajen Russia, Sergei Lavrov a birnin Moscow.Jamil ya kuma sanar da cewar, Russia na cigaba da shirin ta na daukar nauyin taron zaman lafiya tsakanin Gwamnatin Syria da ‘Yan adawar kasar, a Birnin Geneva, dan kawo karshen cigaba da zub da jinin da ake yi a kasar.Minister Lavrov yace, suna cigaba da ganawa da bangarorin biyu, dan shawo kansu su amince su halarci taron kasashen duniya nan ba tare da bata lokaci ba, duk da jan kafar da ‘Yan adawar ke yi.Fira Ministan yace, Russia na kuma nazari dan baiwa Gwamnatin Syria rancen kudade, duk da yake basu cimma matsaya akai ba.Kasashen Yammacin duniya a karkashin Amurka da Britaniya, na adawa da duk wani shiri na baiwa Gwamnatin Syria makamai, inda suka bukaci shugaba Bashar al Assad ya sauka daga karagar mulki.