Masar

Ana huskantar babbar matsala a kasar Masar bayan kashe mutane 10

Hargitsi a kasar Masar
Hargitsi a kasar Masar REUTERS/Stringer

Ana Cigaba da matsin lamba ga shugabanin kasar Masar domin sakin hambararen shugaban Kasar Mohammed Morsi na jam’iyyar ‘ya Uwa Musulmi, ganin yadda ake cigaba da arangama tsakanin masu goyan bayan sa da kuma masu adawa da shi.

Talla

Karawar da bangarorin biyu suka yi jiya, yayi sanadiyar hallaka akalla mutane 10 a yayin da gwamman mutane suka jikkata.

Magoya bayan Morsi sun sha alwashin ganin an mayar da shi karagar mulkin, a dai dai lokacin da sabbin hukumomin ke cewa alkalami ya bushe.

Ma’aikatar kula da harkokin cikin Gida ta kasar ta Masar ta bayyana cewar zata ladabtar da duk wani mutum da ya yiwa Doka Karan tsaye, amma kuma ta bukaci bangarorin biyu da su tabbatar sun zauna lafiya.

Ko da sanyin Safiyar Talata ma an samu kashe akalla mutane 6 bayan da masu hamayya da Morsi suka kai hari wa masu goyon bayan sa.

Akalla dai an bada Rahoton lalata Motoci 16 a wani wuri dake kusa da Jami’ar Azhar.

Har yanzu dai akalla akwai masu goyon bayan Morsi Dubu Daya ko Dubu Bityu dake ci gaba da yin zaman dirshan a dandalin da suke gudanar da zanga-zanga.

Wasu daga cikin su sun kewaye wuraren da suka ga an zub da Jini suna alhinin yanda al’amarin ya auku.

Iyalan Morsi dai a wani taron manema labarai da suka kira, sun lashi Takobin gusrfanar da Sojin kasar Kotu, bisa zarginsu ga kamawa da kuma yin garkuwa da shugaban nasu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.