Isra'ila-Felesdinu

Isra'ila da Falasdinu za su ci gaba da tattaunawa kan samar da zaman lafiya

John Kerry, Saëb Erakat et Tzipi Livni a tattaunawar zaman lafiya
John Kerry, Saëb Erakat et Tzipi Livni a tattaunawar zaman lafiya REUTERS/Yuri Gripas

A rana ta biyu da buda tattaunawa tsakanin Palasdinawa da kuma Isra’ila, wadda ta ruguje shekaru uku da suka gabata, jiya Talata a birnin Washington na kasar Amurka sun shata jadawali mai dauke da yadda tattaunawar za ta kasance.

Talla

A cikin makwanni 2 masu zuwa ne dai bangarorin biyu za su soma tattauwar gadan gadan , ko dai a Isra’ila ko kuma a wani gari da ke yankin Palasdinu.

A wani zaman tattaunawar keke-da-keke da suka gudanar tare da mai shiga tsakani wato Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da ya kai bangarorin biyu ga zaman Teburin shawara, jami’an bangarorin biyu duka sun bayyana cewar lokaci yayi da zasu kwo karshen tankiyar da ke tsakanin su shekaru da dama da suka gabata.

Babban mai shiga tsakani na na kasar Israela Tzipi Livni ta shaidawa Takwaranta na bangaren Palasdinawa cewar a wannan tattaunawar ba suda manufar yin jayayya akan abinda ya shude.

A maimakon hakan inji Tzipi Livni zasu duba mafita, su kuma aiwatar da duk matakin da suka dauka.

Daukacin bangarorin biyu dai sun amince su sake haduwa a cikin Makwanni 2 masu zuwa, kuma sakataren harkokin wajen na Amurka ya tabbatar da hakan.

Yace manufar su itace cimma matakin karshe nan da Watanni 9 masu zuwa.

Ya kara da yin kira ga dukkanin bangarorin da su sasanta juna domin samar da zaman lafiya harma yana bayyana cewar kowane bangare na bukatar taimakon juna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.