India

An dauki nauyin karatun wata dalibar India zuwa Amurka

wata uwa ta dafe kai a cikin Asibitin India da ake kula da lafiya 'yaya mata da aka ci zarafinsu
wata uwa ta dafe kai a cikin Asibitin India da ake kula da lafiya 'yaya mata da aka ci zarafinsu ©Reuters.

Wata karamar daliba a kasar India mai suna Shweta Katti, zata fice daga kasar a wani yanki da mata ke fuskantar talauci da cin zarafi bayan an dauki nauyin karatunta zuwa birnin New York na Amurka. Dalibar tana fatar dawowa India domin ta taimaka ma mata a kauyensu wacce tana cikin jerin ‘yaya mata 25 da zasu tafi karatu a Amurka hadi da dalibar Pakistan Malala Yousufzai da Kungiyar Taliban suka harba saboda adawa da karatun ‘yaya mata.