Pakistan-India

Pakistan ta yi watsi zargin kisan Sojin India a Kashmir

Yankin Kashmir da kasashen India da Pakistan ke takaddama
Yankin Kashmir da kasashen India da Pakistan ke takaddama Reuters

Sojin kasar Pakistan sun musanta zargin kisan dakarun Sojin India guda biyar a wani hari da aka kai a yankin Kashmir. Kakakin Sojin kasar yace babu wani Sojansu da ya keta kan iyakar India. Gwamnatin India d tana zargin Pakistan ne da aikata kisan Sojojin a yankin Jammu da Kashmir inda ministan kasar yace an kai wa Sojojin ne harin kwantar bauna.

Talla

Yankin Kashmir yanki ne da bangarorin biyu ke ikirarin mallakinsu ne  wanda suke takaddama tsawon shekaru 60 da suka gabata.

Wannan harin kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen biyu ke shirin komawa teburin tattaunawa, wanda shi ne karo na farko tun da aka samu sauyin gwamnati a kasar Pakistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.