Afghanistan

An soma yi wa 'yan takarar shugabancin kasar Afghanistan rejista

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai
Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai REUTERS/Mian Khursheed

Yau ne hukumar zaben kasar Afghanistan ta soma yi wa wadanda ke neman tsayawa takarar neman mukamin shugabancin kasar, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Hamid Karzai.

Talla

Zaben, wanda za a gudanar a ranar 5 ga watan Afrilun shekara mai zuwa, kamar yadda kakakin hukumar zaben kasar Noor Muhammad Noor ya sanar a yau litinin, akalla mutane 28 ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.