Bangladesh

Abdul Kadir Mullah na fuskantar hukuncin kisa a Bangladesh

Abdul Kadir Mulla Shugaban  Jam'iyyar Musulmi a  Bangladesh
Abdul Kadir Mulla Shugaban Jam'iyyar Musulmi a Bangladesh

 Mutane kusan miliyan 3 suka mutu a lokacin yakin neman yancin kai daga Pakistan a shekarar 1971,bisa  wannan laifin  ne  kotun a  kasar Bangladesh ta yankewa Shugaban    Jam’iyyar Musulmi  kasar, Abdul Kadir Mullah hukuncin kisa.

Talla

Kotun Kolin kasar Bangladesh, ta yankewa shugaban Jam’iyyar Musulmi kasar, Abdul Kadir Mullah hukuncin kisa, saboda rawar da ya taka lokacin yakin neman Yancin kai daga Pakistan a shekarar 1971.
Wata kotu a watan Fabarairu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai saboda samun sa da laifin, amma sai ya daukaka kara, abinda ya haifar da wannan sabon hukuncin.
Hukumomin kasar sun ce mutane kusan miliyan 3 suka mutu a yakin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.