Iran

Rohani zai nemi hadin kan Duniya game da Iran

shugaban kasar Iran, Hassan Rohani.
shugaban kasar Iran, Hassan Rohani.

Shugaban Kasar Iran, Hassan Rohani ya ce zai yi amfani da taron da za a yi na Majalisar Dinkin Duniya a wannan makon, domin neman hadin kan kasashen Yammacin duniya wajen tattaunawa akan batun shirin nukuliyar Kasar.

Talla

Hassan Rohani ya yi wannan bayani na shi a dai dai lokacin da ya ke shirin halartar taron, inda ya ce zai nuna cewa a shirye ya ke ya tattauna akan batun shirin nukiliyan.

Kasar Iran ta jima tana bayyana cewa shirin mallakar makamashin nukiliyan na lumana ne, kuma shugaba Rohani kamar yadda rahotanni ke nuna, a shirye ya ke ya tabbatar da hakan.

Kasashen yammacin duniya sun kakabawa kasar takunkumai bayan kasar ta ki amincewa da bayyana ainihin shirinta ga duniya, wanda hakan mataki ne da Rowhani ya bayyana a matsayin mai tsauri ganin yadda suke gallazawa ‘yan kasar ta Iran.

Tuni dai kasar Amurka ta bayyana cewa mai yiwuwa shugaba Barack Obama da Rohani su gana a bayan fagen taron na Majalisar Dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.