Masar

An kashe yan sanda 3 a yankin Sinai na kasar Masar

wani shingen tsaro na Sojoji a yankin Sinai na kasar Masar
wani shingen tsaro na Sojoji a yankin Sinai na kasar Masar REUTERS/Stringer

An kashe yan sanda 3 a yankin Sinai na kasar Masar a daidai lokacin da wata kungiyar da ke gwagwarmaya da makamai ta fitar da wani faifan bidiyo

Talla

Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a yankin Sinai da ke kasar Masar a yau litinin, a daidai lokacin da wata kungiyar da ke gwagwarmaya da makamai ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kashe wani kanar na ‘yan sanda a kasar.

Shi dai yankin Sinai, na fuskantar yawaitar hare-hare daga ‘yan bindiga, tun bayan kifar da gwamnatin dimokuradiyya ta kasar ‘yau watanni 3 da suka gabata.

Sakamakon haka yasa yan kungiyar ‘yan uwa musulmi masu goyon bayan hambararen shugaban kasar Mohamed Morsi ke ci gaba da yin fito na fito da gwamnatin mulkin sojan kasar, inda darurukan rayukan jama’a suka salwanta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.