Isa ga babban shafi
Syria

Shugabannin kasashen Larabawa su yi taro kan kasar Syria

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya AFP/Getty Images)

A jiya litanin ne aka gudanar da wani taro tsakanin wasu sarakunan kasashen larabawa su uku, da suka hada da na saudiya, Jodan da kuma Daular larabawa, dangane da rikicin da yaki ci yaki cinyewa na kasar Syriya. An gudanar da wannan taro ne a birnin Jidda na kasar Saudiya tsakanin Sarkin Abdalla na Saudiya, tare da takwaransa na kasar Jodan Abdalla na 2, a daya gefen kuma da yarima mai jiran gadon kasar Abudabi Shekh Mohamed Be Zayes Al Nahyane, babban komadan asskarawan kasar Daular larabawa, a karkashin fadi tashin da kasashen yankin ke yi wajen kawo karshen rikicin kasar ta SyriyaHar ila yau zaman taro da ya hada manyan kasashen larabawan guda uku masu arzikin man Petur a duniya, yazo ne a daidai lokacin da manzon musaman na MDD da kasashen larabawa a Syriya, Lakdar Brahimi ke ci gaba da ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakkiya domin shirya zaman taron samar da zaman lafiya kan kasar ta Syriya da ake sa ran gudanarwa a birnin Geneva, zaman taron da ‘yan adawar kasar suka ce bazasu halarta ba,Ita dai kasar Saudiya ta nutse sosai wajen tallafawa ‘yan adawar dake son kifar da gwamnatin Bashar Al’assad na kasar Syriya, inda ba da jimawa ba ta yi watsi da kujerarta da bata dindindin ba, a komitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, domin nuna bacin ranta kan yadda komitin ya kasa tabuka wani abin azo a gani wajen warware rikice rikicen dake faruwa a yankin gabas ta tsakkiya musamman na kasar SyriyaA wani bangaren kuma Mahukumtan Syriya na zargin Jordan, mai makwabta da kasar, da barin a ratsa kasarta wajen shigar da makamai ga sansanonin da ake horar da yan tawaye a cikin kasar ta Syriya, a yayinda ita kuma Daular larabawa kamar kasar Saudiya ke bada tallafin kudi ga yan adawar kasar. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.