Isa ga babban shafi
India

An sako waso Indiyawa uku bayan yin garkuwa da su a Hong Kong

Firaministan kasar India, Manmohan Singh
Firaministan kasar India, Manmohan Singh REUTERS/Adam Hunger
Zubin rubutu: Mahmud Lalo
Minti 1

An sako wasu Indiyawa uku da aka yi garkuwa da su a yankin Hong Kong dake China yayin da suke ziyarar kasuwanci a yankin.

Talla

Rahotanni sun ce Indiyawan sun kwashe kwanaki uku a hanun wasu ‘yan bindiga da suka tsaresu a kudancin China a ranar Asabar.

Da farko an nemi a biya diyyar miliyan 2.5 na dalar Amurka sai dai hukumomin kasar ta China sun ce ba a biya diyyar ba a takaitaccen bayanin da suka fitar game da garkuwar.

Rahotanni na nuni da cewa mutanen uku na hanun ‘yan sanda bayan sako da aka yi a ranar Litinin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.