Pakistan

Pakistan ta nemi Amurka ta dakatar da kai hare-hare cikin kasarta

Hakimullah Mehsud, shugaban Taliban a Pakistan da Amurka ta ce ta kashe
Hakimullah Mehsud, shugaban Taliban a Pakistan da Amurka ta ce ta kashe REUTERS/Reuters TV/Files

Gwamnatin Pakistan ta yi gargadin cewa, ba za a iya samun zaman lafiya ta hanyar amfani da karfi fiye da kima ba.

Talla

Hukumomin kasar na magana ne a matsayin martani kan kisan da jiregen yakin Amurka masu sarrafa kansu ke kai wa a cikin kasar, inda har ma suka kashe daya daga cikin shugabannin Taliban mai suna Hakimullah Mehsud a karshen makon da ya wuce.

Cikin jawabinsa na farko a bainar jama’a tun bayan kisan da jiragen na Amurka suka yi wa Hakimullah Mehsud, Priministan Nawaz Sharif ya yi Allah wadai da harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.