Iraqi

Mabiya Shi’a suna bukin Juyayi na Ashura a Iraqi

Mabiya Shi'a suna Bukin a ranar Ashura a watan Muharram domin juyayayin mutuwar Imam Hussain Jikan Manzon Allah SAW
Mabiya Shi'a suna Bukin a ranar Ashura a watan Muharram domin juyayayin mutuwar Imam Hussain Jikan Manzon Allah SAW REUTERS/Amit Dave

Mabiya Shi’a daga sassa daban daban na duniya sun halarci garin Karbala domin gudanar da bukin ranar da suke Juyayi da ake kira Ashura, sai dai akwai tsauraran matakan tsaro da aka dauka bayan wani hari da aka kai wa mabiyan na Shi’a da ya hallaka mutane 17 Bagadaza.

Talla

Ashura rana ce da Mabiya Shi’a ke dauka a matsayin ranar bakin ciki domin juyayin mutuwar Jikan Manzon Tsira (SAW). Amma duk shekara ana gudanar da bukin ne cikin fargaba da tashin hankali domin sai an zubar da jini tsakanin mabiya Shi’a da Sunni da ke adawa.

Akwai jerin hare haren Bama bamai da aka kai a wajajen Ibadar ‘Yan Shi’a a yankin arewacin Bagadaza babban birnin Iraqi.

Jami’an tsaron kasar sun ce akwai hare haren bama bamai da aka kai da sanyin safiyar Alhamis a Hafriya wanda ya hallaka mutane Tara tare da raunata wasu da dama.

‘Yan Shi’a suna tururuwa ne a garin Karbala domin karrama Kabarin Imam Hussain Jikan Manzon Tsira (SAW) cikin juyayi wanda aka kashe a zamanin Kalifa Yazid na Umayyawa a tsakanin karni na 680 Miladiya.

Mahukuntan Iraqi sun ce kimanin mutane Miliyan biyu ne suke sa ran za su kawo ziyara a Karbala hadi da mutane kimanin 200,000 daga wajen Iraqi.

Akwai dai mabiya Shi’a da dama a kasashen Iraqi da Iran da Bahrain da Afghanistan da Lebanon da Pakistan da kuma Saudi Arebiya da Syria.

Sai dai kuma a irin wannan rana mabiya Sunni suna gudanar da Azumi ne a ranakun 9 da 10 na watan Muharram inda suke ganin bukin na Shi’a ya sabawa addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.