Isra’ila ta yi watsi da rahotan da ke cewa guba ce ta kashe Arafat
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Kasar Isra’ila, Shimon Peres, ya yi watsi da rahotan binciken da ya nuna cewar guba aka sanyawa tsohon shugaban Falasdinawa, Yaseer Arafat, a matsayin abinda ya hallaka shi.
Peres ya ce bai gamsu da rahotan ba, domin idan ana bukatar kashe Arafat, da harsashi kawai za’ayi amfani da shi a saukake.
A kwanan ne wani bincike da aka gudanar a kasar Switzerland ya bayyana cewa guba aka sanyawa Arafat ya mutu lamarin da ya janyo cecekuce a duniya.
Lamarin har ila yau ya sa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya nemi da a gudanar da kasashen duniya su gudanar da bincike mai zaman kansa domin a gano wake da hanu wajen kashe Arafat.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu